Tinubu ya jajanta wa waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya shafa a Neja

0
79
Tinubu ya jajanta wa waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya shafa a Neja

Tinubu ya jajanta wa waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya shafa a Neja

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika da saƙon ta’aziyya zuwa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja bisa hatsarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Talata a ƙaramar hukumar Mokwa dake jihar.

Jirgin ruwan wanda rahotanni suka bayyana cewa yana ɗauke da mutane 300 yawancin su mata da ƙananan yara ya yi hatsari a kogin Gbajibo.

Yayin da aka ceto mutane 150, an kuma samu gawar mutane 25.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar mutanen da suka mutu a hatsarin kwale-kwale a jihar Neja

A sanarwar da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan fannin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya shafa inda ya yi addu’ar Allah ya jiƙansu.

Shugaban ƙasar ya kuma ba da umarni ga hukumar kula da hanyoyin ruwa ta NIWA da ta binciki musabbabin samun yawaitar hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger da ma kasa baki daya.

“Shugaban kasa Tinubu ya godewa ma’aikatan bada agajin gaggawa wadanda suka taimaka wajen gano ragowar mutanen”, inji sanarwar.

Leave a Reply