Babban matsalar Najeriya shi ne cin hanci da rashawa – Ndume

0
70
Babban matsalar Najeriya shi ne cin hanci da rashawa - Ndume

Babban matsalar Najeriya shi ne cin hanci da rashawa – Ndume

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Mohammed Ali Ndume, ya bayyana damuwarsa kan yadda cin hanci da rashawa ya yi ƙamari a Najeriya.

Da yake magana da manema labarai a Kano a ranar Lahadi, Ndume ya ce cin hanci da rashawa na ci gaba da ƙaruwar a ƙasar saboda ’yan siyasa da suka sace kuɗin jama’a ana girmama su.

Ya ce, “Babban matsalarmu a Najeriya ita ce rashawa. Har yanzu ba mu da dokokin da za su magance cin hanci yadda ya kamata.

“Idan ka ga wani a gwamnati wanda ba ya cin hanci, to shi mutum ne mai tsoron Allah. Idan ba haka ba, a Najeriya, za ka saci kuɗi a yi tafiya a ƙyale ka, har a yaba maka.

“Idan ka shiga wani waje, za ka ga mutane na neman kusantarka, suna girmama ka duk da sun san kuɗin da kake taƙama da su na sata ne.

KU KUMA KARANTA: Sanata Ndume ya gana da shugaban jamiyyar APC na ƙasa

“A Najeriya ne kawai za ka ga mutum wanda bai ajiye kuɗi a jiya ba, amma yau ya sayi motoci 10 ko jiragen sama. Sai kuma ka ji danginsa na cewa Allah Ya albarkaci ɗansu.”

Ndume, ya kuma bayyana cewa ya yi ƙoƙarin ganin an samar da doka kan dukiyar da ba san tushenta ba a Najeriya, amma ƙoƙarin nasa bai yi nasara ba.

Ya taɓa neman tsohon shugaban ƙasa ya sa hannu a dokar, amma ya ƙi amincewa.

“Har yanzu babu doka kan dukiyar da ba a san tushenta ba Najeriya, kuma babu wata doka daga gwamnati kan hakan,” in ji shi.

Sanatan ya kuma nuna damuwarsa kan matsalar yunwa a ƙasar, inda ya yi kira da a ƙara noma don magance wannan matsalar.

“Yunwa na addabar mutane, kuma har yanzu ba mu noma ko da kashi biyar cikin ɗari na gonakinmu. Allah Ya yi wa Najeriya albarkar gonaki masu yawa,” in ji Ndume.

Leave a Reply