No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tsadar Rayuwa: Tinubu ya umarci a taƙaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Najeriya na 64

A karo na 2 a jere, gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar taƙaita shagulgulan bikin samun ‘yancin kan Najeriya da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa saboda halin matsin da ƙasar ke ciki.

A hirarsa da manema labarai yayin baje kolin shagulgulan da aka tsara gudanarwa a ranar bikin samun ‘yancin kan, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume yace gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma ta na tausayawa ‘yan Najeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka takaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamitin tabbatar da bai wa ƙananan hukumomin ‘yancinsu

An taƙaita shagulgula a bikin samun ‘yancin kan Najeriya na 63 a bara inda Sanata Akume, yace ba za a gayyaci shugabannin kasashen ketare ba, saboda halin matsin tattalin arzikin da ƙasa ke ciki.

A yayin ganawar ta jiya Alhamis, Akume yace an yanke shawarar ne a bisa la’akari da halin da kasa ke ciki, don haka Shugaba Tinubu ya amince a takaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Najeriya na 64.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...