Seyi Tinubu ya kai gudunmawar likitoci zuwa Maiduguri

0
10
Seyi Tinubu ya kai gudunmawar likitoci zuwa Maiduguri

Seyi Tinubu ya kai gudunmawar likitoci zuwa Maiduguri

Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya kai gudunmawar ma’aikatan lafiya 50 domin bayar da tallafin jinya ga waɗanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri, Borno.

Tinubu ya bayyana haka ne a wata ziyarar jaje da ya kai wa Gwamna Babagana Zulum, a ranar Juma’a a Maiduguri.

Ya ce an tura ma’aikatan lafiya 50 da aka zaɓo daga jihohin Arewa-maso-Gabas don taimaka wa tawagar likitocin da aiki ya sha kansu a jihar.

KU KUMA KARANTA:Yadda aka toshe ruwan Alau Dam na Maiduguri – Maryam Abacha

“Yanzu haka likitocin su nan sun fara wiki kuma za su kasance tare da ku na ‘yan kwanaki masu zuwa don taimakawa wajen shawo kan lamarin.”

Tinubu ya ce tawagar tare da hadin gwiwar gidauniyar Noella sun ba da tallafin kayayyakin jinya da kuma kayan abinci da ba na abinci ba domin kula da yara da manya 50,000 da bala’in ya shafa.

“Wannan somin-taɓi ne, Ina Mai tabbatar maka da cewa ƙarin taimako ya na nan tafe,” in ji Seyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here