No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 159 a mako guda – Hedikwatar tsaro

Hedikwatar tsaro ta Najeriya a ranar Juma’a ta ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 159 tare da kama 174 a makon da ya gabata.

Daraktan yaɗa labarai na Hedikwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a bayanan da ya fitar kan ayyukan rundunonin soji a Abuja.

Edward Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 188 da aka yi garkuwa da su tare da kama masu shirya satar mai 45 da kuma kama makamai da alburusai.

Ya ce, rundunar soji sun dauki matakai na kawo karshen ayyukan ta’addanci da matsalar tsaro a kasar nan.

KU KUMA KARANTA:Sojoji sun hallaka riƙaƙƙen ɗan ta’adda, Halilu Sububu a Zamfara

Acewarsa, ayyukan sojin suna haifar da sakamako mai kyau.

“Bugu da kari, an tura karin sojoji don tabbatar da an gudanar da zaben jihar Edo ba tare da hargitsi ba.

” Rawar da sojoji ke takawa shi ne na bada goyan baya ga ‘yan sanda wajen kare masu zabe da kuma kawar da masu son tada hankali.”

A Arewa maso gabas, Buba ya ce sojojin rundunar Hadin kai sun hallaka ‘yan ta’adda 41 tare da ceto mutane 48.

Ya ce, ‘yan ta’adda 76 ne suka mika wuya ga sojoji tsakanin 11 ga watan Satumba zuwa 17 ga watan.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...