Mutum 4 sun jikkata a Filato sakamakon rushewar wani gini

0
72
Mutum 4 sun jikkata a Filato sakamakon rushewar wani gini

Mutum 4 sun jikkata a Filato sakamakon rushewar wani gini

Mutane huɗu sun jikkata sakamakon rushewar gini a yankin Ƙaramar Hukumar Riyom da ke Jihar Filato.

Rushewar ginin ya auku ne a kusa da Kwalejin Gwamnati da ke garin Riyom safiyar Litinin, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wani mazaunin garin, Dusu Joseph, ya ce “ba a samu asarar rai ba, amma yawancin waɗanda suka samu rauni ƙananan yara ne kuma an kai su asibiti domin duba lafiyarsu.”

KU KUMA KARANTA: Mutum 3 sun mutu a Legas bayan rushewar gini

Shi kuma wani mai suna Bot Rwang, godiya ga Allah ya yi bisa yadda iyalan da ke cikin gidan da ya ruguje suka tsallake rijiya da baya, babu asarar rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here