Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwanaki 3

0
71
Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwanaki 3

Hukumar NiMet ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwanaki 3

Hukumar kula da yanayin samaniya ta Najeriya, NiMet, ta yi hasashen yanayi na tsawa da ruwan sama daga ranar Talata zuwa Alhamis a faɗin ƙasar.

An fitar da hasashen ne a ranar Litinin a Abuja, inda hasashen ya nuna yanayin tsawa a sassan jihohin Bauchi, Kebbi, Taraba, Kano, Katsina, Adamawa, da Kaduna a safiyar ranar Talata.

A cewar hukumar, ana sa ran za a yi tsawa a duk faɗin yankin a cikin wannan ranar.

“A yankin Arewa ta tsakiya, ana sa ran tsawa a sassan jihohin Kogi, Benuwe, Filato, Babban Birnin Tarayya Abuja, Nasarawa da Neja da safe.”

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama a Nijar ya rusa masallaci mai ɗimbin tarihi

Hukumar ta yi hasashen tsawa a sassan jihohin Taraba, Adamawa, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano da Kaduna a safiyar Laraba.

A cewar NiMet, ana sa ran za a yi tsawa a sassan jihohin Borno, Gombe, Adamawa, Taraba, Kano, Katsina da Kebbi da yammacin ranar.

“A yankin Arewa ta tsakiya, ana iya samun tsawa a sassan babban birnin tarayya, Kogi, Neja da Kwara da safe.”

Leave a Reply