Na damu matuƙa da tserewar ‘yan Boko Haram daga kurkuku, sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri — Zulum

2
38
Na damu matuƙa da tserewar 'yan Boko Haram daga kurkuku, sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri — Zulum

Na damu matuƙa da tserewar ‘yan Boko Haram daga kurkuku, sakamakon ambaliyar ruwa a Maiduguri — Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ya shiga damuwa kan yiwuwar wasu kwamandojin Boko Haram sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar sakamakon ambaliyar ruwa da ta auka wa garin Maiduguri.

Ambaliyar ruwan dai ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar.

A cewar rahotanni, ambaliyar ruwan ta lalata wani ɓangare na tsohon gidan fursin inda aka ɗebe ɗaurarru da dama zuwa sabon gidan fursin matsakaici a Maiduguri.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da hakan ga wakilin Daily Trust.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba, sun ce yayin da aka kwashe wasu daga gidan kurkukun, wasu kuwa sun tsere.

Yayin da aka tambaye shi, ko yana damuwa kan cewa wasu shugabannin Boko Haram ka iya tserewa, sai Gwamnan Zulum ya mayar da amsa da cewa ya damu.

KU KUMA KARANTA:Ambaliyar Ruwa: Mutane miliyan 1 sun shiga wani hali – Zulum

Ya ce, “Ina damuwa, eh, ina damuwa matuka. Amma ya kamata kasa a ran ka cewa gwamnatin jihar Borno ta kafa inda ‘yan tada kayar baya zasu tuba. Shekaru 2 da suka gabata, Mayakan Boko Haram da iyalansa 200, 000 suka tuba, kuma ina tunanin hakan yana haifar da sakamako mai kyau wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali”

Zulum ya kuma koka kan yadda jihar ta sake samun kanta cikin annoba a yayin da take fuskantar matsalar tsaro.

“Zan iya tunawa, an kashe sama da mutane dubu 300, an lalata dubban ajujuwa na karatu, ‘yan tada kayar baya sun lalata daruruwan wurare.

”Muna ta kokarin fita daga wannan matsalar, yanzu kuma ga wani bala’in”.

2 COMMENTS

  1. Aslm Mai girma gwanma dakace kadamu da guduwar yan boko haram, maiyasa ba’a kashesuba lokacin da akakamasu aikaga da ankashesu kota hanyar gana musu azaba dabaka shiga cikin damuwarba. Saboda haka inamai baka shawara idan ansake kama wasu gaskiya babu amfanin barinsu a raye ngde

  2. Aslm Mai girma gwanma dakace kadamu da guduwar yan boko haram, maiyasa ba’a kashesuba lokacin da akakamasu aikaga da ankashesu kota hanyar gana musu azaba dabaka shiga cikin damuwarba. Saboda haka inamai baka shawara idan ansake kama wasu gaskiya babu amfanin barinsu a raye ngde

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here