Shugaba Tinubu ya naɗa sababbin shugabannin tsaro na DSS da NIA
Daga Idris Umar, Zariya
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin manyan daraktoci na hukumar leƙen asiri ta Ƙasa, NIA, da hukumar tsaro ta DSS.
An naɗa Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon Darakta-Janar na NIA, ya yin da Adeola Oluwatosin Ajayi shi ne sabon Darakta-Janar na DSS.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar.
Sanarwar ta ce: “Ambasada Mohammed ya yi fice a hidimar kasar waje tun lokacin da ya shiga NIA a shekarar 1995. Ya yi ayyuka daban-daban, har ya kai ga kara masa girma zuwa mukamin Darakta da kuma nadin sa a matsayin shugaban hukumar ta Najeriya zuwa Libya.
“Wanda ya gama karatu a Jami’ar Bayero Kano a shekarar 1990, ya yi aiki a kasashen Koriya ta Arewa da Pakistan da Sudan da kuma a fadar gwamnati da ke Abuja.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya naɗa sabon Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida
“Sabon Darakta-Janar na DSS, Mista Adeola Ajayi, ya kai matsayin mataimakin darakta Janar na Hukumar.
Ya yi aiki a lokuta daban-daban a matsayin Darakta na Jiha a Bauchi, Enugu, Bayelsa, Ribas, da kuma Kogi.
“Sabbin naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da shugabannin NIA da DSS suka yi a baya bayan nan.
“Shugaba Tinubu yana sa ran sabbin shugabannin tsaro za su yi aiki tukuru don sake canza hukumomin leƙen asirin guda biyu don samun sakamako mai kyau tare da Tuhumar su da su kawo kwarewarsu wajen tinkarar kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan ta hanyar inganta hadin gwiwa da hukumomin ‘yan uwa da kuma yin aiki tare da jami’an tsaron Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).
“Shugaban ya gode wa Daraktocin manyan hukumomin leƙen asirin guda biyu masu barin gado bisa ayyukan da suke yi wa ƙasa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.”