No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan bindiga a Kaduna sun yi garkuwa da Hakimi tare wasu mutane 5

Wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da hakimin Garu Kurama da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna, Yakubu Jadi, da ɗiyarsa Malamar Cocin Katolika da wasu mutane huɗu a ƙauyan Gurzan Kurama.

Duk da cewa rundunar ‘yansandan Kaduna ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ƙungiyar jama’ar Kudancin Kaduna (SOKAPU), ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a Josiah Abraks, ta bayyana cewa an yi garkuwa da mutanen ne a daren Juma’a, 23 ga Agusta, 2024, amma har yanzu ‘yan bindigar ba su nemi dangin waɗanda sukai garkuwa da su ɗin ba.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar wani basarake da ‘ya’yansa

SOKAPU, ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ban tsoro tare da ƙira ga hukumomin tsaro da sauran wanda abin ya shafa da su yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin an sako waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin cikin gaggawa.

Kazalika ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma inda ta buƙaci jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi ko yunƙuri da ba su a saba gani ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...