‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar wani basarake da ‘ya’yansa

0
79
‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar wani basarake da 'ya'yansa

‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar wani basarake da ‘ya’yansa

Daga Idris Umar, Zariya

‘Yan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a ƙauyen Galadimawa da ke ƙaramar hukumar Igabi, a jihar Kaduna.

Miyagun ‘yan bindigan sun yi awon gaba da matar basaraken ƙauyen tare da ‘ya’yansa guda biyu a yayin harin, ‘yan bindigan waɗanda suka je da niyyar su sace basarsaken ne a harin da suka kai cikin dare sai ba su tarar da shi ba

Mutanen da ‘yan bindigan suka sace sun haɗa da matarsa Fatima Aliyu da ƴaƴansa, Abdullahi Aliyu da Kamal Aliyu.

‘Yan bindigan masu yawan gaske sun fara harbe-harbe bayan sun isa ƙauyen domin tsoratar da mutane kafin su fasa katanga domin shiga gidan basaraken.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Isa Bawa 

Sarkin Fadan Galadimawa, Hussaini Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Talata, inda ya nuna matuƙar damuwa.

Ya bayyana cewa an ji maharan suna tambayar inda gidan basaraken yake, wanda hakan ke nuna cewa sun zo ne musamman domin su sace shi amma ba su same shi ba.

Malam Umar ya ci gaba da bayanin cewa ‘yan bindigan sun yi ɓarna a gidan ciki har da lalata silin ɗin gidan bayan sun haura ta katanga.

Da ba su samu basaraken ba, sai suka yi awon gaba da matarsa ta biyu da ƴaƴansa biyu.

Mun so jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, kan lamarin.

Amma  bamu sameshi ta waya ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here