Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

0
139
Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Matar da ta fi tsufa a duniya ta rasu

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya, ‘yar kasar Spain, Maria Branyas Morera, wacce aka haifa a Amurka kuma ta ga ‘yan duniya biyu, ta mutu tana da shekaru 117, in ji danginta.

“Maria Branyas ta bar mu. Ta mutu kamar yadda ta yi fata: wato a lokacin da take barcinta, cikin kwanciyar hankali kuma ba tare da jin raɗaɗi ba,” kamar yadda danginta suka rubuta a shafinta na X a ranar Talata.

“Za mu riƙa tunawa da ita saboda nasiharta da kyautatawarta,” in ji su.

KU KUMA KARANTA: Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Issa Hayatou, ya rasu

Branyas, wacce ta rayu tsawon shekaru 20 da suka gabata a gidan kula da tsofaffi na Santa Maria del Tura da ke garin Olot a arewa maso gabashin Spain, ta yi gargadi a cikin sakon da ta wallafa cewa tana jin “raunana”.

“Lokacina ya kusa. Kada ku yi kuka, ba na son a zubar min hawaye. Kuma kar ku wahalar da ni. Duk inda na je, zan yi farin ciki,” ta faɗa a shafin nata wanda iyalanta ke kula da shi.

Guinness World Records a hukumance ya amince da matsayin Branyas a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a cikin watan Janairun 2023 bayan mutuwar Bafaranshe Lucile Randon mai shekara 118.

Bayan mutuwar Branyas, mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya shi ne Tomiko Itooka dan kasar Japan, wanda aka haife shi a ranar 23 ga Mayun 1908 kuma yana da shekaru 116 a duniya, a cewar ƙungiyar bincike kan tsofaffi ta Amurka.

Maria Branyas Morera ta ce tsawon rayuwar da ta samu yana da alaƙa ne da rashin ɗaukar rayuwa da zafi da kula da lafiyar ƙwaƙwalwarta da ta jiki da kuma yin alaƙa mai kyau da mutane.

A yanzu bayan mutuwar Branyas, wani ɗan Japan Tomiko Itooka mai shekara 116 ne zai zama mutum mafi tsufa a duniya.

Leave a Reply