Tinubu ya bada umarnin biyan tallafin man fetur

0
217
Tinubu ya bada umarnin biyan tallafin man fetur

Tinubu ya bada umarnin biyan tallafin man fetur

Daga Ali Sanni Larabawa

Shugaba Bola Tinubu, ya amince wa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), da yayi amfani da ribar shekarar 2023 da aka samu domin biyan tallafin man fetur.

Shugaban ya kuma amince da dakatar da biyan riba da aka samu a 2024 ga gwamnati don taimakawa da kuɗaɗen da kamfanin zai kashe.

Ko da yake Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawa a kan tallafin.

Sai dai, gwamnatin tarayya ta sha musanta biyan tallafin.

Idan ba a manta ba, ‘yan Najeriya sun yi zanga-zanga saboda wahalar da ake ciki a ƙasar, kuma ɗaya daga cikin buƙatunsu shi ne a dawo da tallafin man fetur.

KU KUMA KARANTA: Gayawa ‘yan Najeriya gaskiya gamaida tallafin man fetur – Bode George

Amma a cikin wani jawabin da Tinubu yayi, ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur ba zai yiwu ba, inda ya bayyana cire tallafin a matsayin abu mai wahala amma kuma wajibi ne gwamnatinsa tayi.

Ya ce tallafin ya kasance tamkar wata sarƙa data ɗaure tattalin arziƙin ƙasar.

A ranar Litinin, wata jarida a Intanet ta ruwaito cewa Tinubu ya amince wa NNPCL da ya biya tallafin bayan da kamfanin ya koka cewa ya yi amfani da duk hanyoyin da zai iya don samar da isasshen man fetur a ƙasar nan amma hakan ya gagara.

Ƙoƙarin ya haɗa da ƙara yawan samar da mai ta hanyar yaƙi da satar mai da lalata bututun mai; sake tsara bashi, jinkirta biyan ’yan kwangila, ’yan kasuwa da ayyukan daba su da muhimmanci.

NNPCL ta  shaida wa shugaban cewa waɗannan ƙoƙarin sun gaza warware matsalar da ake fuskanta, kuma idan ba a biya tallafin ba, kamfanin ba zai iya sanya kuɗin da ake buƙata daga gare shi ga asusun gwamnatin tarayya ba.

Don haka, Tinubu ya umarci kamfanin da ya yi amfani da haraji da sauran kuɗaɗen da aka ware wa gwamnatin tarayya domin biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.

Rahoton ya ce an bayar da wannan umarni ne a ranar 6 ga watan Yuni, 2024.

Hasashen da NNPCL ya yi, ya nuna cewa jimillar kuɗaɗen tallafin man fetur daga watan Agusta 2023 zuwa Disamban 2024 zai kai Naira tiriliyan 6.884, wanda zai hana kamfanin biyan Naira tiriliyan 3.987 na haraji da kuɗaɗen haƙƙin mai ga asusun gwamnatin tarayya.

Leave a Reply