Ina fuskantar barazana akan aiki na – Ministan Lantarki
Daga Ali Sanni Larabawa
Ministan lantarkin Najeriya, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa akwai masu yi masa barazana kan aikin da yake yi.
Ministan ya bayyana cewa yana samun barazanar ne daga mutanen dake adawa da cigaban da yake kawowa ɓangaren wutar lantarki.
Adebayo ya ƙara da cewa a cikin ƙasa da shekara ɗaya da yayi a ofis an ƙara ƙarfin wutar lantarki 1,000MW da ƙasar ke samarwa
Ministan ya ce yana samun kiraye-kirayen barazana daga wasu ɓoyayyun mutane waɗanda ke adawa da ci gaban da ake samu a ɓangaren wutar lantarki.
KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga: Gwamnan Kano ya roƙi Gwamnatin tarayya ta rage farashin man fetur da na lantarki
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a jihar Oyo cikin shirin ‘Political Circuit’ na tashar Fresh FM.
Ministan yace duk matsalolin da ake fuskanta a fannin wutar lantarki abu ne wanda za’a iya magancewa.
“Za’a samu turjiyar, mutane zasu yi ƙoƙarin kawo maka cikas, masu yin zagon ƙasa da sauransu. A karon farko bari na faɗi cewa na samu kiraye-kiraye na barazana.” “Ni ne ministan lantarki na 49 a Najeriya.
Akwai yiyuwar sauran ministocin da suka gabace ni an hana su yin aikinsu yadda ya dace. Ba talakawa ba ne ke lalata turaken wutar lantarki da ababen fashewa.”
“Laifi ne wanda aka tsara. Aiki ne na iyayen daba. Dukkaninmu ƴan Najeriya ne amma mun san abin da wasu daga cikinmu za su iya aikatawa.”
Da yake ƙarin haske game da gagarumin ci gaban da aka samu a shekara ɗaya da yayi a kan kujerar minista, yace Najeriya da ƙyar take iya samar da wutar lantarki mai ƙarfin 4,000MW.
Ya ƙara da cewa cikin ƙasa da shekara daya da yayi a ofis, tsare-tsaren da ya kawo sun sanya an samu ƙarin sama da 1,000MW.
Adebayo Adelabu ya bayyana cewa yanzu wuta ta kara samuwa a sassan ƙasar nan biyo bayan shirin gwamnati.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sanya wasu matakai da za su tabbatar da wadatar hasken wutar lantarki a ƙasa.