Gwamnan Neja, shugaban kiristoci sun yi Alla-wadai da bankawa coci wuta

0
100
Gwamnan Neja, shugaban kiristoci sun yi Alla-wadai da bankawa coci wuta

Gwamnan Neja, shugaban kiristoci sun yi Alla-wadai da bankawa coci wuta

Daga Ali Sanni Larabawa

An banka wa cocin na Christian Church of God wuta a kan titin Kwalejin Ilimi mai zurfi ta tarayya da ke Kontagora a ranar Asabar, kuma akayi wawason kayan ciki.

Gwamna Umar Bago na jihar Neja, ya fusata tare da yin kakkausar suka ga waɗanda suka banka wa Cocin Redeemed wuta a Kontagora .

Gwamna Bago yace wannan ɓarna rashin hankali ne da rashin mutunci.

An ruwaito cewa an taɓa banka wa cocin wuta shekaru 10 da suka wuce, bayan wasu ɓata garin yara sun yi barazanar rashin amincewa a ƙarasa ginin cocin.

KU KUMA KARANTA: Aƙalla mutum 20 sun mutu a Bayelsa bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta

Shugaban ƙungiyar Kiristocin jihar Neja, Bulus Yohanna ya yi tir da wannan barnar.

Yohanna ce dabbanci ne kuma bai kamata ba. Kuma ya yi ƙira ga gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki tare da kamo waɗanda suka yi wannan aika-aikar. “Tunda akwai dokar ‘yancin kowa ya yi addininsa a faɗin Najeriya.

Cocin dai kamar yadda Mataimakin Faston, Samson Ogbebor ya bayyana takai kimanin shekaru 20 da ginawa.

Leave a Reply