No menu items!

Sample Page Title

Date:

’Yan bindiga a Taraba sun harbe matafiya 7 a hanya

Mahara sun harbe matafiya bakwai har lahira a safiyar Litinin a kan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke Jihar Taraba.

Mahara sun harbe wasu matafiya guda bakwai har lahira a safiyar Litinin a kan babbar hanyar Takum zuwa Wukari da ke jihar Taraba.

Kisan gilla da aka yi wa matafiyan da direban motarsu ya haifar da zaman ɗar-ɗar a yankin Takum.

Shaidu sun bayyana wa wakilinmu cewa ɗauƙacin matafiyan waɗanda ’yan garin ne, suna hanyarsu ta zuwa garin Sa’ayi da ke Jihar Binuwai ne lokacin da harin ya rutsa da su a tsakanin garin Chanchangin da garin Wukari.

Wani shaida ya ce maharan sun buɗe wa motar wuta ne suka kashe duk mutanen da ke cikinta, nan take, amma ba su ɗauki komai ba a cikinta.

KU KUMA KARANTA: Mutane 9 ne suka mutu a rikicin ‘yan bindiga a Libya

Ya yi zargin maharan na daga cikin ’yan ta’addan da suka addabi dazukan da ke tsakanin Jihar Binuwai da Jihar Taraba.

A bisa wannan hanya ce dai aka kashe basaraken garin Chanchangi da babban ɗansa a watan Yuli.

Hanyar ta zamo tarkon mutuwa saboda ayyukan ’yan ta’adda da ke yin fashi da kuma garkuwa da matafiya domin karɓar kuɗin fansa a cikin dare da yini.

An tuntuɓi kakakin ’yan sandan jihar Taraba, DSP kwach,  game da harin na safiyar Litinin, amma jami’in ya ce masa sa zai bincika.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...