Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da Garo a kotu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 57

0
130
Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da Garo a kotu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 57

Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da Garo a kotu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 57

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da sabuwar ƙara na tuhumar tsohon Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da Murtala Sule Garo da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da Naira biliyan 57.4.

A cewar takardar ƙarar, ana tuhumar Murtala Garo da Lamin Sani da Muhammad Takai da haɗa kai wajen aikata laifi da zanba-cikin-aminci da gabatar da bayanan ƙarya da badaƙalar kuɗaɗe.

KU KUMA KARANTA;Gwamnatin tarayya zata biya Julius Berger biliyan 280 don kammalan titin Abuja zuwa Kano

Gwamnatin na zarginsu da wawure kuɗin ƙananan hukumomi da ke asusun haɗaka tsakanin jihar da ƙananan hukumomi 44.

Sannan ana zargin badaƙalar kuɗi ta Naira Biliyan 57.4 da suka karkatar da su zuwa asusun ajiya na ƙashin kai.

Haka kuma ana zargin sun sauya kuɗin zuwa Dalar Amurka.

Haka kuma, gwamnatin na tuhumar su da mallakar kadarori da kuɗaɗen a ƙasar Dubai da Otel a garin Abuja da wasu gidajen mai a Kano.

Gwamnatin dai ta ce za ta gabatar da shaidu 143 a gaban kotun a lokacin shari’ar.

Leave a Reply