Hatsarin jirgin ruwa ya laƙume rayukan mutane 9 a Zamfara
Masu aikin ceto a hatsarin Jirgin Ruwa da ya faru a ƙauyen Kali na Ƙaramar Hukumar Gumi a Jihar Zamfara, sun tabbatar da tsamo gawarwaki guda tara na mutanen da hatsarin Jirgin ruwa ya rutsa da su a yankin.
Lamarin dai ya faru ne sanadiyyar firgici da tashin hankalin da alummar suka shiga sakamakon samun labarin yunƙurin ‘yan bindiga na aukawa garin domin kai masu hari.
A hirar shi da manema labarai, Aliyu Sukata Kali, Sarkin Jirgin Ruwa na yankin kuma matuƙin Jirgin da ya samu hatsarin ya bayyana yadda lamarin ya faru.
“Abin da ya faru shi ne, an ce ɓarayi sun kawo kusa da garin mu, hakan ya sa jama’a suke ta tururuwa suna barin garin inda muke fiton su da jirgin ruwa. Mun ɗauki sawu na biyar kusan mutun hamsin, mun kai tsakiyar ruwa sai jirgin ya nutse”
Yace ganin hakan ya sa suka yi kururuwa suna neman agajin al’umma, inda masu aikin ceto fiye da mutun ɗari suka auka cikin ruwan wasu akan gora wasu akan masaki, wasu kuma suna kurma ihu suka dinga ceto mutane har aka fitar da mutun arba’in yayin da aka samu gawarwakin mutane tara. Sai wani mutun ɗaya da yanzu haka yake a asibiti, rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Ƙasimu Umar, wani shaidar gani da ido, kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka yi aikin ceton mutanen, ya ce lokacin da lamarin ya faru sun yi gudu ne, suna kan tsauni domin tsira da rayukan su daga harin na ɓarayin daji, kamar yadda su ka saba duk lokacin da suka ji sammatar ɓarayin. Ya ce, a wannan karon sun bar iyalan su da ‘ya’yan su suna baya hakan ya sa ba su wuce ba, su ka tsaya su jira isowar su.
KU KUMA KARANTA;Gwamna Lawal ya rattaɓa hannu akan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a Zamfara
Ya ce “Ɗaya daga cikin mu da ya lura jirgin zai nutse, sai ya auka a cikin ruwan domin ya jawo igiyar jirgin, amma kafin ya samu nasarar yin hakan sai jirgin ya nutse, kaya kawai ake gani a saman ruwa”.
A nata bayanin, Malama Amina ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto bayan nutsewar jirgin tace sun shiga ruɗani da tashin hankali a lokacin da jirgin ya nutse kafin a samu nasarar ceto su.
Ta ce sun shiga jirgin ne tare da yaranta biyar kuma an ceto su duka, yanzu haka suna karɓar magani a wani asibiti da ke yankin.
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Zamfara, kuma Ɗan Majalisar da ke wakiltar yankin, Hon Adamu Aliyu Gumi, ya bayyana takaicin aukuwar lamarin, nan take ya kuma ba da kuɗi domin sayo waɗansu jiragen ruwan kasancewa wannan ce kaɗai hanyar da al’ummar ke iya fita garin.
Shi dai yankin na Kali da ke gundumar Birnin Magaji a Karamar Hukumar Gummi ta jihar Zamfara, yana ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, da lamarin ya daidaita su, bugu da ƙari, yankin na da matuƙar wahalar shiga saboda rashin hanya da ƙalubalen tsaro.
To Sai dai Allah ya albarkaci ƙauyen na Kali da maƙwabtan shi da albarkatun noma masu tarin yawa, da suka haɗa da Gero da Dawa da wake da Kwarya da Dankali da dai Sauran su. Suna kuma noma sau biyu a shekara, noman rani da na damina.