No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan sanda a Gombe sun kama mutum 90 kan zargin sace kayan jama’a a lokacin zanga-zanga

Wasu al’ummar Bolari na jihar Gombe sun dawo da kayayyakin da ɓata-gari suka sace a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa

’Yan sanda sun jinjina wa al’ummar yankin Bolari  bisa yadda suka dawo da kayayyakin da ɓata-gari suka sace a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Rundunar ’Yan sandan jihar Gombe ta yaba musu ne a lokacin da take sanar da kama mutum 90 kan zargin sace kayan jama’a a yayin zanga-zangar.

Rundunar ta ƙara da cewa an samu nasarar dawo da wasu kayayyaki masu yawa da aka sace  a jihar ba tare da asarar rai ba.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Gombe, ASP Buhari Abdullahi, ya sanar da cewa a halin yanzu zaman lafiya ya dawo a jihar inda kowa ke ci gaba da gudanar da harkokinsa na yau da kullum.

Ya ja hankalin jama’a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu, suna masu kara kulawa ta musamman da duk abin da su amince da shi ba.

A cewar sanarwar, dawowar zaman lafiya na nuna kwarewa, juriya, da hakuri da jami’an rundunar da sauran hukumomin tsaro suka yi a jihar.

Sannan ya ce kowa ya ba da gudummawa wajen wannan zaman lafiya, yana mai rokon jama’a da cewa su ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro wajen kiyayewa da tabbatar da doka da oda.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...