Jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga a Najeriya

0
192
Jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga a Najeriya

Jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa ta janye tallafin man fetur ne a yunƙurinta na bunƙasa tattalin arzikin ƙasar da kawar da masu yi mata “zagon-ƙasa” duk kuwa da raɗaɗin da hakan ke haifarwa ga ‘yan ƙasar.

Shugaban ya bayyana haka ne ranar Lahadi a jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya ta gidan talbijin na ƙasa, kwanaki huɗu bayan ‘yan ƙasar sun tsunduma cikin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Babbar buƙatar masu zanga-zargar ita ce gwamnati ta dawo da tallafin fetur, wanda suka ce cire shi ne ya jefa ƙasar cikin ƙarin matsin rayuwa.

A jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya taɓo batutuwa da dama da matakan da ya ce gwamnatinsa tana ɗauka domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.

Ga manyan batutuwan da Shugaba Tinubu ya faɗa:
Na ji ciwon irin asarar rayuka da aka yi a wasu jihohi, irin su Borno, Jigawa, Kano, Kaduna da dai sauransu, da ɓarnata dukiyoyin jama’a a wasu jihohin, kai har ma da yadda aka riƙa wawushe manyan kantuna da shaguna, saɓanin alƙawarin da masu shirya zanga-zangar suka yi cewa, zanga-zangar za ta kasance cikin lumana a faɗin ƙasarmu.

A matsayina na shugaban wannan ƙasa, wajibi ne na tabbatar da doka da zaman lafiya. Kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya ɗora min alhakin hakan kuma na amince, da cewa zan kare rayuka da dukiyoyin kowane ɗan ƙasa, don haka gwamnatinmu ba za ta saka ido ta bar wasu tsiraru masu ɓoyayyiyar manufa ta siyasa su wargaza wannan ƙasa mai albarka ba.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya amince da a sayarwa Ɗangote matatar man fetur

A wannan yanayi da ake ciki, ina ba masu shirya wannan zanga-zangar da ma masu yinta umarni, da su dakatar da duk wata zanga-zanga, su maye gurbinta da buɗe ƙofar tattaunawa da sulhu, wanda a ko da yaushe ƙofata a buɗe take ga hakan.

Na tsinci kaina a yanayin da ba ni da zaɓin da ya wuce na ya ɗauki matakin da ya dace duk da raɗaɗinsa, don haka na cire tallafin man fetur da kuma kawar da tsarin musayar kuɗaɗen waje da yawa waɗanda suka haifar da tsaiko da cikas ga tsarin tattalin arzikin ƙasarmu da ci gabanta da namu.

Waɗannan matakai da na ɗauka sun toshe duk wata ribar da ’yan fasa-ƙwauri da masu yi wa ƙasarmu zagon-ƙasa suke samu.

Haka kuma sun toshe tallafin da muka bai wa ƙasashen da ke maƙwabtaka da mu na a-sai-da-rai-a-nemo-suna, da tuni kafin mu farga sun mayar da tattalin arzikinmu kashin-baya.

E! Na yarda, hakan zai haifar min da ƙalubale. Amma ina tabbatar muku cewa na shirya fuskantar kowane irin ƙalubale muddin zai samar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar Najeriya.

Mun fitar da sama da Naira biliyan 570 ga jihohi 36 domin faɗaɗa shirye-shiryensu na tallafa wa rayuwar al’ummomin jihohinsu, yayin da ƙananan ‘yan kasuwa 600,000 suka ci gajiyar tallafinmu, ana sa ran ƙarin ƙananan ‘yan kasuwa 400,000 su ma za su amfana.

Gwamnatinmu ta bai wa matasa kulawa ta hanyar kafa tsarin rance ga ɗalibai mai suna NELFUND.

Yanzu haka an fitar da kuɗi da ya kai Naira biliyan 45.6 ga ɗalibai da cibiyoyinsu daban-daban, kuma ina kira tare da ƙarfafa gwiwa ga ƙwararrun matasanmu da su yi amfani da damarsu wajen cin gajiyar shirin.