Ana ci gaba da samun asarar rayuka a Najeriya sakamakon zanga-zanga

0
21
Ana ci gaba da samun asarar rayuka a Najeriya sakamakon zanga-zanga

Ana ci gaba da samun asarar rayuka a Najeriya sakamakon zanga-zanga

Matsalar rashin tsaro wadda tana ɗaya daga cikin abubuwan da suka tunzura ‘yan Najeriya su fito yin zanga zanga na ci gaba da ɗaukar rayukan jama’a musamman a arewacin ƙasar.

Wannan na zuwa ne lokacin da ‘yan ta’adda suka hallaka mutane goma sha uku ciki har da jami’an tsaron al’umma biyar a Sakkwato, a wasu hare hare biyu da suka kai cikin kwana uku.

Daga cikin matsalolin da ‘yan Najeriya ke yi wa zanga zanga akwai matsalar rashin tsaro wadda ta jima tana addabar jama’a kuma ta yi sanadin salwantar rayuka da dukiyoyi, kuma ƙoƙarin da mahukunta ke yi ya ƙasa daƙile matsalar.

Wani abu da ke tabbatar da ci gaba da wanzuwar matsalar shi ne wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, yankin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka mutane da dama.

Kantoman ƙaramar hukumar Umma Maikano ya ce ‘yan bindigar sun kai harin ne ranar Asabar da ta gabata suka harbe manoma shida, inda biyar suka mutu, kuma kwana biyu bayan wannan harin suka dawo suka yi wa jami’an tsaron al’umma kwanton ɓauna suka kashe mutane takwas haɗi da jami’an su biyar.

KU KUMA KARANTA;Ɗaruruwan mutane sun fito zanga-zanga a birnin tarayya Abuja (Hotuna)

Wannan zanga zangar dai da ta shigo kwana na biyu yau ita ma ta zama sanadin salwantar rayukan wasu jama’a a wasu jihohin Najeriya kamar yadda wasu bayanai da ma hotuna suka nuna a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

A jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya ma bayanai sun nuna a garin Yauri jami’an tsaro na ‘yan sanda sun yi harbi akan masu zanga zangar har an samu salwantar rayuwa, da kuma raunuka.

Muryar Amurka ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi a kan wannan batun na harbi lokacin zanga zanga amma kakakin bai ɗauki ƙiran ba.

Duk da yake yau ne rana ta biyu ta zanga zanga, jama’a ba su fito ba a jihar Sakkwato inda a Kebbi an samu fitowar jama’a a Birnin Kebbi sai dai ba kamar rana ta farko ba, kuma duk da haka al’amurra sun soma daidaita, inda masu shaguna sun soma buda wuraren sana’ar su kuma jama’a na ci gaba da lamurran su cikin lumana, amma duk da haka jami’an tsaro na ci gaba da sintiri a manyan tituna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here