Ana gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya

0
52
Ana gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya

Ana gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya

Dubban mutane a birane daban-daban na Najeriya sun soma gudanar da zanga-zanga domin bayyana ɓacin ransu kan matsin rayuwar da suke ciki wanda ya yi ƙamari tun hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki a shekarar 2023.

Masu zanga-zangar, wadda ta ja hankalin ‘yan ƙasar tun da aka sanar da ranar gudanar da ita, sun fantsama kan tituna a manyan birane irin su Lagos da Kano da Abuja.

Suna riƙe da kwalaye da aka yi rubutu kamar “A kawo ƙarshen yunwa a Najeriya”, “A dawo da tallafin man fetur” da sauransu.

Sai dai bayanai daga sassa da dama sun nuna cewa mutane suna fuskantar katsewar intanet da ƙira a wayoyinsu.

A Abuja, babban birnin Najeriya, masu zanga-zangar sun hau manyan tituna duk da umarnin da wata kotu ta bayar na taƙaita zanga-zangar a Babban Filin Wasa na Ƙasa.

KU KUMA KARANTA: An taƙaita wuraren da masu zanga-zanga za su bi a Abuja

Lauyan masu zanga-zangar, Barista Deji Adeyanju, ya shaida wa manema labarai cewa bai ga umarnin da kotun ta bayar ba, amma duk da haka yana rarrashin masu zanga-zangar su gudanar da ita a wurin da kotun ta iyakance musu.

Kwamishinan ‘yansandan Abuja, Benneth Igweh, ya gargaɗi masu zanga-zangar kan rashin bin umarnin kotun, yana mai cewa sun ɗauki dukkan matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

A Lagos, babban birnin kasuwanci na ƙasar, masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna a yankin Ikeja inda suka nufi gidan gwamnati domin bayyana rashin jin daɗinsu kan matsin rayuwar da ake ciki.

A Kano, dandazon mutane sun hau kan tituna suna zanga-zanga inda suka riƙa ƙira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan kawo sauƙi ga rayuwarsu.

An jibje jami’an tsaro a birane daban-daban domin sanya ido da tabbatar da ganin an gudanar da zanga-zangar cikin oda.