No menu items!

Sample Page Title

Date:

Turkiyya ta la’anci kisan gilla da aka yi wa shugaban Hamas

Turkiyya ta la’anci kisan gilla da aka yi wa shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai Iran.

“Muna la’antar kisan gilla ga Shugaban Siyasar Hamas Ismail Haniyeh a wani mummunan hari a Tehran,” in ji sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a safiyar Laraba.

“Wannan hari na da manufar yaɗa rikicin Gaza a dukkan yankin. Idan ƙasashen duniya ba su ɗauki matakan dakatar da Isra’ila ba, yankinmu zai fuskanci manyan rikice-rikice,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: An kashe shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Iran

“An sake nuna cewar gwamnatin Netanyahu ba ta da niyyar rungumar zaman lafiya.”

Ma’aikatar ta ƙara da cewa “Muna miƙa saƙon ta’aziyya ga jama’ar Falasɗinawa da suka sadaukar da dubban ɗaruruwan shahidai irin su Haniyeh don ganin sun zauna lafiya a ƙasarsu, ƙarƙashin inuwar ƙasa mallakinsu.”

Turkiyya ta yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan “buƙatun jama’ar Falasɗinu.”

Haniyeh, fitaccen ɗan siyasar Falasɗinu da ƙungiyar gwagwarmaya, ya kasance babban jigo kafin da lokacin yaƙin kisan kiyashin Isra’ila a Gaza da aka mamaye.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...