Ba mu san abin da masu zanga-zanga suke buƙata ba – Gwamnonin APC
Daga Idris Umar, Zariya
Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana cewa ba su san ainayin maƙasudin da ya sa ake shirin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan ba.
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya musamman matasa na yin gangami domin gudanar da zanga-zanga a faɗin kasar nan daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agustan 2024.
Da yake jawabi bayan wani taron sirri na ƙungiyar gwamnonin da aka gudanar a Abuja, Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce “Ba mu san abin da suke buƙata ba a shirin su na gudanar da zanga-zanga, kamata yayi su zo domin mu tattauna a kan al’amurran da ke faruwa domin samar da mafitar da ta dace.
KU KUMA KARANTA: Tinubu na ganawar sirri da gwamnonin APC
“Mu a matsayinmu na ƙungiya mun himmatu wajen ganin an haɗa kan Kasar nan, duk wani abu da zai sa ‘yan Najeriya su yi rayuwa mai inganci za mu samar da shi, da ya haɗa da ayyukan yi ga Matasa maza da mata waɗanda suka kammala karatu”.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, bai dace ba a halin yanzu kasar nan a yi wata zanga-zanga, ina kira ga ƴan Najeriya da su soke shirin gudanar zanga-zangar da aka shirya yi.
Ya kuma bukaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri da Gwamnati, yana mai cewa ana kokarin ganin an gyara matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a ƙasar.
“Wannan shi ne domin mu samu mu iya tafiyar da ƙalubalen rashin tsaro, da kalubalen mafi karancin albashi na ƙasa, da kalubalen samar da abinci, sannan kuma ga gwagwarmayar ƙoƙarin fita daga koma bayan tattalin arziki da ake ciki a yanzu”.
“Muna amfani da wannan dama wajen baiwa yaranmu maza da nata shawara da su guji tunzura wanda ka iya haifar da rikici ko hargitsi a kasar,” inji shi.
Tun baya mu ƴan Nijeriya muna fama da ƙalubale da dama a sabili da taɓarɓarewar tattalin arzikin duniya, da rashin tsaro a Najeriya, da rikicin siyasa, da yakin neman zabe, ga jam’iyyun adawa na kai suka a kafafen Sada Zumunta na zamani kan manufofin Gwamnati daban-daban.
“Muna so mu ba da shawara don maslahar ƙasa, kuma a matsayin mu masu kishin ƙasa, dole ne ƴan ƙasa suji cewa Najeriya ƙasar su ce, domin ba mu da wata ƙasa da za mu iya ƙira tamu bayan Najeriya.”