No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mutum 3 sun mutu a Legas bayan rushewar gini

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mutum uku a lokacin da wani gini ya rufta a rukunin gidajen Arowojobe da ke yankin Maryland a jihar.

Da yake tabbatar wa kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN, rushewar ginin, Babban sakataren hukumar, Dakta Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Alhamis.

Ya ce mutane ukun da suka mutu a lokacin faruwar lamarin duka ma’aikatan gini ne.

“Bayan samun labarin faruwar lamarin, jami’an hukumarmu sun gazaya wurin tare da gaggauta fara aikin ceto, inda suka zaƙulo gawarwakin mutum uku duka maza, da wasu mazan biyu da aka zaƙulo da ransu sai kuma wani mutum guda da ya maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin da shi ma aka ceto shi”, in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Ya kuma ƙara da cewa tuni aka garzaya da mutanen da aka ceto zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Tuni aka kai manyan motocin tono domin faɗaɗa aikin ceton.

Ko a farkon wannan wata ma, an samu ruftawar ginin wata makaranta a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar yara fiye da 20, tare da raunata gommai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...