Ɗan Majalisar Wakilai ya yi wa ‘yarsa kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

0
132
Ɗan Majalisar Wakilai ya yi wa 'yarsa kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

Ɗan Majalisar Wakilai ya yi wa ‘yarsa kyautar mota don murnar kammala karatun sakandire

Mamba mai wakiltar mazaɓar Pankshin/Kanke/Kanam, Yusuf Gagdi, ya baiwa ‘yarsa kyautar dalleliyar mota ƙirar Lexus RX, crossover SUV, domin murnar kammala karatun sakandire tare da samun maki mai kyau a jarrabawarta ta shiga jami’a, UTME.

‘Yar ta sa mai suna Aisha Gadgi ta kammala karatunta a makarantar Lead British International School Abuja ranar Asabar.

Wani shahararre a Facebook, Saminu Maigoro, ya wallafa hotunan matashiyar tare da mahaifinta, suna baje kolin motar ta alfarma.

“Ina taya Aisha Yusuf Gagdi murnar kammala karatunki a makarantar Lead British International School Abuja. Allah Ya sa hakan ya zama mafarin ci gaban ki a rayuwa.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Abba ya raba wa ƙananan manoma kyautar takin zamani

“Don murnar kammala karatun ta da kuma rawar da ta taka a JAMB, mahaifinta ya ba ta mamaki da kyautar mota,” in ji Mista Maigoro.

Sai dai kuma kyautar ta janyo cecekuce a shafukan sadarwa, inda wasu su ke goyon bayan hakan, wasu kuma su ke alla-wadai duba da matsin rayuwa da ƴan Najeriya ke ciki.

Leave a Reply