Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano – SEMA

0
60
Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano - SEMA

Ambaliyar ruwa ta lalata ƙananan hukumomi 3 a Kano – SEMA

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), ta bayyana cewar ambaliyar ruwa ta lalata wasu yankuna a ƙananan hukumomin Sumaila, Kibiya da Tudun Wada a jihar.

Sakataren hukumar, Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi ne, ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki.

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMET), ta yi gargaɗin cewar akwai ƙananan hukumomi 14 a jihar da ka iya fuskantar ambaliyar ruwa.

SEMA, ta ziyarci yankuna da abin ya shafa don tantance irin ɓarnar da ruwa ya yi tare da miƙa rahoto ga gwamnatin jihar don ba su tallafi.

Hukumar za a tabbatar da adadin mutane ko gidajen da abin ya shafa bayan haɗa rahoton.

KU KUMA KARANTA:NIMET ta yi hasashen ambaliyar ruwa a Kano

Kwanan nan, SEMA da sauran masu ruwa da tsaki sun ziyarci yankunan da ake tsammanin fuskantar ambaliya don wayar musu da kai dangane da hatsarin da ke tattare da madatsar ruwa ta Tiga.

A yayin wannan ziyara, an wayar da kan al’ummar yankunan kan yadda za su shawo kan ambaliya.

SEMA ta bayar da shawar gina madatsar ruwa ta wucin gadi don kare waɗannan yankuna.

Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ta bayar da tallafi ta hanyar bai wa mazauna yankunan horo da kuma tallafin kuɗi.

Ko’odinetan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Dokta Nura Abdullahi, ya jaddada muhimmancin sarrafa shara yadda ya dace don kaucewa aukuwar ambaliyar ruwa, musamman a birane.

Ya yi kira ga jama’a su daina zubar da shara a magudanan ruwa.

Taron, wanda UNICEF ta tallafa, ya haɗa da wakilai daga ƙungiyoyi daban-daban a jihar.

Leave a Reply