Yadda katsewar intanet ta shafi sassan duniya
Katsewar intanet a sassan duniya ta haifar da tarnaƙi inda aka dakatar da tashin jirage, ayyukan bankuna suka tsaya yayin da wasu aikace-aikacen asibitoci ma suka tsaya cik.
Kamfanin CrowdStrike mai tsaron yanar gizo a ranar Juma’a ya ce ba batu ne na tsaro da ya shafi kutse ba.
Kazalika matsalar ta shafa har da wasu kafafen yaɗa labarai waɗanda suka kasa watsa shirye-shiryensu.
A cewar AP, kamfanin na CrowdStrike ya ce ana kan shawo kan matsalar.
KU KUMA KARANTA:CBN ya ba bankuna umarnin saka sabon harajin tura kuɗi
Sai dai sa’o’i bayan sanarwa da kamfanin ya fitar, an lura cewa matsalar ta ƙara ta’azzara.
A filayen tashin jirage a Amurka, da nahiyar turai da Asiya, rahotanni sun ce an ga dogayen layuka bayan da masu tarbar fasinjoji suka tsaya cik da ayyukansu sanadiyar wannan matsala.
A Australia, matsalar ta tilastawa kafofin yaɗa labarai tsayar da shirye-shiryensu.
A Afirka ta Kudu, ayyukan bankuna sun tsaya sanadiyyar wannan katsewa yayin da a New Zealand hanyoyin biyan kuɗaɗen da ke amfani da kati suka samu tangarɗa.