No menu items!

Sample Page Title

Date:

SSANU da NASU na ci gaba yin zanga-zanga a Abuja

Daga Idris Umar, Zariya

A halin yanzu dai mambobin ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da na (NASU) sun hallara a Unity Fountain da ke Abuja, suna zanga-zangar ƙin biyansu albashin watanni huɗu.

Shugaban SSANU Mohammed Aruna Ibrahim da babban sakataren NASU, Comrade Peters Adeyemi ne ke jagorantar zanga-zangar.

Ƙungiyoyin biyu dai sun ji haushin cewa, duk da umarnin da shugaban ƙasa ya bayar na a biya basussukan watanni huɗu, mambobin ƙungiyar malaman jami’o’in (ASUU) ne kawai aka biya, inda suka bar SSANU da NASU ba su biya ba.

KU KUMA KARANTA: SSANU da NASU sun yi zanga-zangar lumana a jami’ar ABU

Sai dai kuma, an yi wata arangama a Unity Fountain yayin da jami’an tsaro masu tsauri suka hana masu zanga-zangar ficewa daga wurin taron.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...