No menu items!

Sample Page Title

Date:

Su wa suka yi wa Ɗan-Bilki Kwamanda duka?

Daga Idris Umar, Zariya

Fitaccen mai sukar gwamnatin nan Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda ya karɓi na jaki bayan da wasu waɗanda ake tunanin hukumar tsaro ne suka kama shi da zargin zagin gwamnan Kaduna Malam Uba Sani.

Dattijon mai shekaru kusan 70 ya sha dukan ne a daren jiya bayan da ya shiga hannu.

Da fari sun tambaye shi shi ɗan wace jiha ce? ya ce Kano, suka ce me ya haɗa shi da Kaduna yake zagin Gwamnan su, sai ya kaɗa baki yace shi ɗan Najeriya ne kuma ɗan Arewa, faɗar haka ke da wuya aka fara zane shi da bulala.

KU KUMA KARANTA: Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Duk da ya yi ta roƙon su yana cewa yana da ciwon suga, hawan jini da zuciya bai sa sun sassauta wajen zuba masa bulala ba inda suka umurce shi da ya rusuna sannan suka ci gaba da zuba masa bulala inda kuma an ka saka masa ankwa a hannu.

An zarge shi ne da cin mutuncin Gwamnan jihar Kaduna a lokuta da dama.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...