Ƙungiyar ƙwadago ta amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci

0
64
Ƙungiyar ƙwadago ta amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci

Ƙungiyar ƙwadago ta amince da N70,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan Nijeriya.

Ministan Labarai, Mohammed Idris ne ya sanar hakan yau Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu wanda ya sanar da hakan yayin taron da ya yi da shugabannin ƙungiyar ƙwadago, ya kuma ƙuduri aniyar bitar dokar albashi mafi ƙaranci duk bayan shekara uku.

“Muna farin cikin sanar da ku a yau [Alhamis] cewa ƙungiyoyin ƙwadago da Gwamnatin Tarayya sun amince da ƙarin albashin N62,000.

“Sabon mafi ƙaranci na ƙasa da ake sa ran shugaban ƙasa zai miƙa wa Majalisar Tarayya shi ne N70,000,” in ji Idris.

KU KUMA KARANTA: Tinubu zai gana da ƙungiyar ƙwadago kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata

Kazalika, Shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo da Ministan Ƙwadago Nkiruka Onyejeocha, da sauran jami’an ɓangarorin biyu sun tabbatar da batun ministan.

A cewar Kwamared Ajaero, sun amince da tayin shugaban ƙasar ne saboda yarjejeniyar ta ƙunshi wani gwabi musamman bitar dokar albashi mafi ƙanƙanta duk bayan shekaru uku.

Wannan na zuwa ne bayan kwashe tsawon lokaci ana taƙaddama tsakanin ’yan ƙwadago da Gwamnatin Tarayya game da sabon albashin mafi ƙanƙanta ga ma’aikata.

Tun ba yanzu ba dai ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa wajibi ne Gwamnatin Nijeriya ta yi wa ma’aikata ƙarin albashi domin ya yi daidai da halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar ya yi a ranar da ya karɓi mulki cikin watan Maris na shekara ta 2023, ya sanya farashin kayan masarufi ya nunnunka, lamarin da ya jefa al’ummar ƙasar cikin mummunan hali.

Leave a Reply