An ba ’yan Arewa kwana 4 su fice a yankin jihar Delta

0
71
An ba ’yan Arewa kwana 4 su fice a yankin jihar Delta

An ba ’yan Arewa kwana 4 su fice a yankin jihar Delta

An ba al’ummar Arewa wa’adin kwana huɗu su fice daga garin Abavo da ke Jihar Delta.

Fadar sarkin garin ce Abavoa ta sanar da wa’adin a ranar Litinin, kuma zai kare ranar Alhamis.

Sarkin Hausawan garin, Usman Alhassan ya ce, ba zato ba tsammani masarautar ta aiko musu su cewa, “dole ne sai mun bar garinsu, kuma wani ma baya da kudin motar da zai koma gida.

“Wasu ba su da ma kudin cin abinci ballantana na mota, kwana husu suka ba mu, daga Litinin zuwa Alhamis,” kamar yadda BBC ta ruwaito shi.

Sarkin Hausawan ya ci gaba da cewa wa’adin barin garin Abavoa da aka ba ’yan Arewa ya jefa su cikin tashin hankali.

Ya bayyana cewa yawancinsu sun riga sun tare a Abavo tare da matansu da ’ya’yansu, kuma sun fi shekara 30 a garin.

Sarkin ya ce, “Akalla Hausawan da ke garin nan sun kai mutum 200, muna sana’ar kayan abinci da nama, wasu kuma leburori ne.”

KU KUMA KARANTA: Za a fuskanci yunwa mai tsanani a arewa maso gabashin Najeriya – Majalisar Dinkin Duniya

Ya ce, “Maganar ta zo daga fadar sarki, yaron sarki ne ya zo ya gaya mana.

“Mun je domin jin ba’asi sai suka ce mana ana sace mutanensu ana neman kuɗin fansa, kuma suna zargin mutanenmu.”

Wani dan majalisar masarautar ya bayyana cewa, “An ɗauki matakin ne saboda yawan garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da ake yi a garin.”

Amma Sarkin Hausawa ya bayyana cewa a iya saninsa da kuma matsayinsa, ba a taɓa kama wani Bahaushe da sunan ya aikata laifi ba.

Ya ce, “Mun kai 30 muna zaune garin nan, wasu Sakwkwatawa wasu Kanawa wasu kuma Katsinawa ne wasu kuma ’yan Taraba ne.”

Koda yake, Malam Aliyu Yahya, wanda shi ne limamin gari na Abavo, ya shaida wa BBC cewa suna fadi-tashin ganin an samu maslaha.

Limamin garin ya kara da cewa suna kokarin kwantar wa ’yan Arewa hankali da tare da kira gare su, “su bi duk hanyoyin da ya kamata domin samun nasara kan lamarin.”

Liman Aliyu ya ce sanin kowa ne cewa dokar Najeriya ta ba kowane dan kasa damar zama a inda yake so ba tare da tsangwama ba.

Kakakin ’yan sanda jihar Delta, SP. Bright Edafe, ya ce ba shi da labarin wa’adin da masarautar garin na Abavo ya ba ’yan Arewa.

Ya ƙara da cewa babu wani mahaluki da ke da ikon tayar da wani dan Najeriya daga wani yanki a ƙasar ta wannan hanyar.