No menu items!

Sample Page Title

Date:

Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 48 a Gaza a ƙasa da awa ɗaya

Isra’ila ta kai hare-hare ta sama guda uku cikin ƙasa da awa ɗaya waɗanda suka kashe Falasɗinawa aƙalla 48 a Gaza, a cewar rundunar kare fararen-hula ta yankin.

Isra’ila ta ce ta ta kai hare-hare biyu waɗanda rundunar kare fararen-hula ta ce sun jikkata mutanen da dama.

Wasu sabbin alƙaluma da aka fitar sun nuna cewa mutum 25 sun mutu a makarantar Al Razi da ke cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat na tsakiyar Gaza wadda ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda shugaban makarantar Mohammed al Mughair ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

KU KUMA KARANTA: Jami’ai a Gaza sun zaƙulo gawawwakin Falasɗinawa 21 daga cikin ɓaraguzai

Kazalika dakarun Isra’ila sun kashe aƙalla mutum 18 sannan suka jikkata mutum 25 a harin da suka kai garin Al Mawasi da ke kusa da birnin Khan Younis na kudancin Gaza.

Haka kuma sun kashe mutum biyar da ke tsaye a kusa da wani shatale-tale a garin Beit Lahia da ke Gaza, a cewar wasu jami’ai.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...