‘Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara

0
99
'Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara

‘Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara

’Yan bindiga sun sako mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara, da suka yi garkuwa da ita.

Mawaƙin da kansane ya sanar da hakan tare da wallafa hotonsa tare da ita bayan an sako ta; kimanin kwana 20 ke nan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da dattijuwar a gidanta da ke Karamar Hukumar Danja a Jihar Katsina.

A cikin bidiyon, an ga Rarara zaune a kusa mahaifiyar tasa, yana rungume da ita

Ya kuma bayyana bayyana godiyarsa ga Allah da ya kungiyar da mahaifiyar tasa, tare da mika godiya ga mutane da suka taimaka da addu’o’i a kan lamarin.

A ranar 28 ga watan Yuni, 2024, ’yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifiyar Rarara, inda daga bisani suka buƙaci kuɗin fansa Naira biliyan ɗaya.
Daga baya sun rage kuɗin zuwa miliyan 900.

An yi garkuwa da Hajiya Halima  ne a ranar 28 ga watan Yuni, a gidanta da ke yankin Kahutu a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mutum 2 da ake zargin sace mahaifiyar Rarara

Shaidu a ƙauyen sun ce da misalin karfe ɗaya na dare ne dandazon ’yan bindiga suka kutsa gidan dattijuwar suka yi awon gaba da ita.

“A kafa suka zo, ba su yi harbi ba a lokacin da suka kai harin suka yi garkuwa da ita cikin ’yan mintoci.

“Dattijuwar ba ta bijire musu ba  a lokacin da suka memi ta biyo su.

“Duk da cewa ’yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kaɗai suka ɗauka.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ’yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda bindigogin da suke dauke da su,” in ji wani mazaunin kauyen na Kahutu.

Ya ce, “Watakila maharan sun bar baburansu ne daga nesa suka tako zuwa cikin kauyen a kafa.

“Muna rokon Allah Ya kubutar da ita cikin koshin lafiya domin tana taimaka mana sosai a wannan kauyen.

“Danta Rarara mai yawan taimakon al’umma ne, kuma ya kawo mana abubuwan cigaba sosai a garinmu,” in ji shi.

Leave a Reply