Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

0
99
Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Kotu ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

Wata Babbar Kotun jihar Kano ta haramta wa Aminu Ado Bayero ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano.
Alƙaliyar Kotun Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ce ta bayar da umarnin a zaman da ta yi ranar Litinin.

Kazalika ta haramta wa sarakuna huɗu da gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙira ayyana kawunansu a matsayin sarakunan Bichi, Gaya, Karaye da Rano.

Da ma dai tuni gwamna Abba Kabir Yusuf ya rusa dokar da ta ƙirƙiri masarautun nasu, sannan ya dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano da Kakakin Majalisar Dokoki da sauran ‘yan majalisar dokokin jihar ne suka shigar da ƙara a gaban kotun ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida Esq, ranar 27 ga watan Mayu inda suka nemi ta hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan ƙiran kansu a matsayin sarakuna.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero

Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu ta ce Majalisar Dokokin jihar Kano tana da ikon yin kwaskwarima ga dokokin jihar domin tabbatar da zaman lafiya kamar yadda ta yi wa dokar masarautun jihar gyaran fuska.

Kotun ta gargaɗi ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su guji yin duk wani abu da zai ci karo da Dokar Masarautu ta Jihar Kano (da aka rusa) ta 2024.

“Ina umartar dukkan sarakunan da aka rusa masarautunsu su miƙa kayan da ke hannayensu waɗanda suka kasance mallakin Masarautun Kano ga gwamnatin jihar,” in ji Mai Shari’a Adamu-Aliyu.

Leave a Reply