Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

0
114
Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

Bankin duniya ta baiwa Togo kyautar dala miliyan 200 don magance matsalar lantarki

Bankin Duniya ta amince da bai wa Togo dala miliyan 200 don magance matsalar samar da wutar lantarkin da kasar ke fama da ita na tsawon watanni.

A dai-dai lokacin da za a fara babban zaɓen ƙasar, a ƴan watannin nan, Togo na fuskantar matsananciyar matsalar rashin wutar lantarki, lamarin da ya haddasa tsadar rayuwa a ƙasar.

Ministan tattalin arziki da kuɗin Togo, Sani Yaya, ya bayyana farin cikinsu game da samun wannan tallafi, sannan ya ce kudin zai agaza wurin gina manyan layin wuta wanda hakan zai taimaka wa ƴan ƙasar da ke rayuwa a ƙauyuka wajen samun wutar cikin sauƙi.

Ministan ya ƙara da cewa wannan tallafi zai sa sama da mutane miliyan ɗaya da rabi su samu wutar lantarki mara katsewa.

KU KUMA KARANTA: Bankin Duniya na gargaɗi kan ‘matsananciyar yunwa’ a Gaza

Matsalar ƙarancin wutar da aka fuskanta na zuwa ne bayan Najeriya wacce ita ce ke bai wa Togon da Nijar da kuma Benin lantarki ta bayyana takaita adadin wutar da za ta dinga ba su a ranar 1 ga watan Mayun shekarar nan.

Hukumar da ke kula da wutar lantarkin ta ce Najeriya wacce ita ce ta fi ba su wutar na bin su bashin miliyoyin daloli na lantarkin da suka sha kuma suka kasa biya.