Gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da Hakimai daga hannun sarkin musulmi

0
50
Gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da Hakimai daga hannun sarkin musulmi

Gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da Hakimai daga hannun sarkin musulmi

A ƙarshe dai gwamnan Sakkwato ya karɓe ikon naɗa sarakuna da suka haɗa da uwayen ƙasa da hakimai daga hannun mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Wannan ya biyo bayan rattaɓa hannu da gwamnan ya yi ga dokar da Majalisar ƙananan hukumomi ta yi wa gyaran fuska.

Duk da yake an samu ƙorafe-ƙorafe da dama har daga manyan mutane akan ƙudurin gwamnatin Sakkwato na yin gyaran fuska ga dokar ƙananan hukumomi wadda daga cikin tanadin ta, akwai ikon naɗa uwayen ƙasa da hakimai, yanzu maganar ta zo ƙarshe, domin ƙudurin ya zama doka.

Sai dai saɓanin yadda mutane suka ɗauka a farko na ganin an rage wa sarkin musulmi ƙarfin iko, gwamna Ahamd Aliyu yace, ai an sha yin gyare-gyare ga dokoki a jihohi har ma da jihar Sakkwato.

Yace ba a yi wannan don cin zarafi ko ƙuntata wa wasu jama’a ba, sai dai don kawo ci gaba ga jama’ar Sakkwato.

Wannan dokar dai tana nufin yanzu Sarkin Musulmi ba shi da ikon naɗa sarakuna a ƙananan hukumomi, kamar yadda mataimakin mai tsawatarwa na Majalisar dokokin jihar sakkwato ɓangaren masu rinjaye Abubakar Shehu Yabo yace.

KU KUMA KARANTA:Ranar Lahadi ce 1 ga watan Muharram – Sarkin Musulmi

Wasu masu ruwa da tsaki a masarauta sun nuna rashin jin daɗin su a kan wannan dokar yayin da wasu suka ja hankalin gwamnati a kan ta nada Sarakuna wadanda suka mutu ba’a sake yin su ba.

Shi kuwa Malami Waziri ya bayyana ra’ayi ne cewa, yanzu dai a iya cewa takun saƙa a harkar masarauta a Sakkwato ta zo ƙarshe, domin an rufe wannan shafi, iko ya koma a hannun gwamna.

Yanzu hankali ya koma jihar Kano wadda yanzu haka ke da Sarakuna biyu, inda ake dakon ganin yadda za ta kaya, da ma jihohin Katsina da Kebbi, da su ma ke takun saka a kan sarauta.