Kotu ta ba da belin tsohon ministan lantarki
Saleh Mamman ya gurfana a gaban kotu ne a bisa tuhume-tuhume 12 dake da nasaba da haɗa baki domin halasta kuɗaɗen haram da mallaka tare da amfani da kuɗaɗen ta haramtacciyar hanya.
Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ya ba da belin tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman, akan kuɗi Naira biliyan 10 da mutum 2 da za su tsaya masa suma akan makamancin wannan adadi kowannen su.
Da yake zartar da hukunci akan buƙatar ba da belin wanda ake ƙara, Mai Shari’a Omotosho ya bayyana cewa wajibi ne waɗanda za su tsaya masa su kasance sun mallaki kadarori a Abuja da darajarsu ta kai aƙalla naira miliyan 750.
KU KUMA KARANTA:Ministan Lantarki na Najeriya ya yi barazanar ƙwace lasisin kamfanonin rarraba wuta
Haka kuma kotun ta ƙara da cewa wajibi waɗanda za su tsaya masan su miƙa sahihan takardun kadarorin gareta tare da shaidar biyan haraji ta shekaru 3.
Har ila yau kotun ta buƙaci wanda ake karar ya gabatar mata da bayanan banki da takardun tafiye-tafiyensa.
A maimakon hakan, kotun ta bayyana cewar wanda ake ƙarar na iya samar da takardar banki mai dauki da adadin kuɗin da ta yanke a matsayin jingina kuma idan ya yi hakan ba sai ya samar da masu tsaya masa ba.
Daga bisani kotun ta ɗage zamanta zuwa ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa domin fara sauraron ƙarar.
Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Alhamis Mai Shari’a Omotosha, ya ba da umarnin adana Saleh Mamman a gidan gyaran hali na Kuje har sai an kammala sauraron buƙatar ba da belinsa.