Gwamna Lawal ya rattaɓa hannu akan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a Zamfara

0
44
Gwamna Lawal ya rattaɓa hannu akan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a Zamfara

Gwamna Lawal ya rattaɓa hannu akan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a Zamfara

A ranar Alhamis, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaɓa hannu akan dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Suleiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis, inda yace majalisar tsaron jihar ta yanke shawarar taƙaita zirga-zirgar baburan ne a yayin wani taron gaggawa da ya gudana a Larabar da ta gabata.

Gwamnan ya sanya hannu akan dokar ne a fadarsa da ke Gusau, babban birnin jihar.

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Zamfara ya jinjinawa jami’an tsaro tare da yin jaje ga wanda iftila’in ya shafa

An ruwaito sanarwar na cewa, “yau, gwamna Dauda Lawal ya rattaɓa hannu akan dokar da ke taƙaita ko haramta zirga-zirgar babura daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safiya a ko’ina a faɗin jihar.

“Hakan wani yunƙuri ne na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da daƙile kalubalen tsaro da fadada matakan da gwamnati ke ɗauka wajen yaƙi da matsalar ‘yan bindiga da sauran nau’ukan laifuffuka a jihar.

“An baiwa antoni janar na jihar zamfara ikon gurfanar da duk wanda ya sabawa dokar a gaban ƙuliya.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here