Wata makaranta a Jos ta rushe da ɗalibai suna zana jarabawa

0
90
Wata makaranta a Jos ta rushe da ɗalibai suna zana jarabawa

Wata makaranta a Jos ta rushe da ɗalibai suna zana jarabawa

Ginin makarantar sakandaren Kent Academy ya rushe da ɗalibansa a yayin da suke rubuta jarabawa a garin Jos na Jihar Filato.

A halin da ake ciki dalibai da dama sun makale a cikin baraguzan ginin makarantar mai hawa biyu da ke unguwar Busa Buji a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a 12 ga watan Yuli, 2024.

Tuni jami’an tsaro da jami’an gwamnati da al’ummar gari suka isa wurin inda suka dukufa gudanar da aikin ceto daliban da abin ya ritsa da su.

KU KUMA KARANTA: Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wakilinmu ya bayyana cewa an samu nasarar zakulo wasu daga cikin ɗaliban, inda aka garzaya da waɗanda suka samu rauni zuwa asibiti.

Ana kuma farganar samu asarar rai, amma ba a kai ga gano adadin ba, ko aka sanar a hukumance.

Ƙarin bayani na nan tafe…….

Leave a Reply