Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama’a

0
50
Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama'a

Faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza bayan ba da umarnin kwashe jama’a

An gwabza ƙazamin faɗa da ruwan bama-bamai a birnin Gaza da wasu yankunan Falasɗinawa a yau Juma’a yayin da masu shiga tsakani ke ci gaba da kokarin dakatar da yakin da ya shiga cikin wata na goma.

Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa a taron Ƙungiyar Tsaro ta NATO a birnin Washington jiya Alhamis cewa jami’an diflomasiyyar Amurka, duk da matsalolin da ake fuskanta, suna samun “ci gaba” tare da masu shiga tsakani na ƙasa da ƙasa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tare da jaddada cewa “lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen wannan yaƙi”.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza

Kafofin yaɗa labarai masu alaƙa da mahukuntan yankin Hamas, sun ce sojojin Isra’ila sun ƙaddamar da sabbin hare-haren sama fiye da 70.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutum 32, tana mai cewa “an kai waɗanda suka mutun, waɗanda akasarinsu yara da mata ne zuwa asibitoci cikin dare, saboda kisan kiyashin da ake ci gaba da yi”.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana kuma gwabza faɗa a yankin Rafah da ke kudancin ƙasar, inda dakarunta suka “kawar da ‘yan ta’adda da dama a hare-hare ta sama”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here