No menu items!

Sample Page Title

Date:

‘Yan ta’adda sun kashe mutane sama da mutum 7,000 a Yammacin Afirka a bana – Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana buƙatar gaggawa wajen haɗa kai don yaƙi da ta’addanci da sauran matsaloli na rashin tsaro a Yammacin Afirka.

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Tuggar ya ce daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2024, an samu hare-haren ‘yan ta’adda 800 a Yammacin Afirka, musamman a ƙasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.

Ya ƙara da cewa sama da mutane 7,000 ne suka mutu sakamakon hare-haren na ta’addanci a yankin.

KU KUMA KARANTA: Bai kamata ƴan ba-ni-na-iya su shigo da matsalolinsu Gabas ta Tsakiya ba – Turkiyya

“Dole ne mu haɗa kai waje guda don magance matsalolin tsaro, kuma mu yi aiki ba gajiyawa domin tabbatar da tsaro, dimokuraɗiyya da cigaban yankinmu,” in ji Tuggar.

Ya ƙara da cewar a yayin taron, sun kuma sake nazari da duba kan Tsarin Dimokuraɗiyya da Shugabanci na ECOWAS, inda ya kuma yaba da ayyukan samar da zaman lafiya da taimakon jinƙai da ake bayarwa a yankin.

Ƙasashen Yammacin Afirka dai suna fama da hare-hare na ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ISIS da Boko Haram ko ISWAP.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...