MƊD za ta tallafa wa dubban ƴan Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita

0
71
MƊD za ta tallafa wa dubban ƴan Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita

MƊD za ta tallafa wa dubban ƴan Sudan da yaƙi ya ɗaiɗaita

Hukumar Kula da Ƴan gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za ta faɗaɗa ayyukanta na bai wa ƴan gudun hijira agaji zuwa ƙasashen Libya da Uganda, inda a yanzu haka dubban ƴan Sudan suka kwarara bayan sun tsere wa ƙazamin yaƙin da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasarsu da ƴan tawayen RSF.

Shirin tallafa wa masu gudun hijirar na Sudan da hukumar UNHCR ta wallafa ya yi hasashen cewar ƴan gudun hijirar Sudan dubu  149,000 za ta  karɓa a Libya, kafin ƙarshen shekarar bana, yayin da take sa ran wasu ƙarin ƴan Sudan ɗin dubu 55 za su tsere zuwa Uganda duk da cewa babu iyaka tsakaninsu.

KU KUMA KARANTA: Ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi na fuskantar tsananin rayuwa shekara guda da soma yaƙi

Ƙididdigar Majalisar Ɗinkin Duniya ta baya-bayan nan ta nuna cewar, ƴan Sudan akalla dubu 20 ne suka tsere zuwa Libya a shekarar da ta gabata, yayin da ƴan gudun hijirar Sudan dubu 39 suka tsere zuwa Uganda tun bayan ɓarkewar rikicin da ya tagayyara ƙasar.

Wannan sabon al’amari na zuwa a yayin da alkaluma suka nuna cewar, tuni Sudan ta zama ƙasa ta farko a duniya mafi fama da matsalar yawan waɗanda da suka rasa muhallansu, adadin da ya kai mutane kimanin miliyan 12 a cikin ƙasar, yayin da wasu ƙarin miliyan biyu suka tsere zuwa ƙasashe makwafta.

Leave a Reply