Halin da na shiga bayan karɓar kwangilar abincin bogi – Hajiya Aisha Ibrahim (Bidiyo)
Wata mata mai gidan abinci ta faɗa tarkon ’yan damfara inda aka ba ta kwangilar bogi ta samar da abinci na kwanaki uku kan kuɗi Naira miliyan 13.
An ba Hajiya A’isha Ibrahim kwangilar bogin ce da sunan za ta ciyar da mabuƙata dubu tara a ƙananan hukumomi uku na jihar.
Labarin Hajiya Aisha da ke sana’ar abinci a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ya karaɗe gari ne bayan ta yi bidiyon halin da take ciki a kafofin sada zumunta.
Hakan ya sa gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulqadir Muhammad ya shiga tsakani ya biya ta kuɗin data kashe wajen yin abincin, aka karɓi abincin aka raba wa masu buƙata.
A zantawar datayi da manema labarai, Hajiya Aisha ta ce wani mutum ne ya tuntuɓe ta da ya ba ta kwangilar samar da abinci ga mutane 9,600 a ƙananan hukumomin Bauchi, Alkaleri, da Kirfi.
A yayin da take bayyana irin halin da ta shiga, duk da cewa ba ta bayyana sunan mutumin da ya ba ta kwangilar bogin ba, Hajiya Aishah ta ce mutumin ya ba ta tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a rattaba hannu kan yarjejeniyar kwangilar, kuma ba za a saka ta cikin hadari ba.
“Ya dage cewa in ci gaba da kwangilar saboda ba a sanya hannu kan yarjejeniyar ba, amma za a ba ni takardan yarjejeniyar yin kwangilar lokacin da aka sanya hannu,” inji Aisha.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta fara farautar ma’aikatan da suke da shaidar karatun bogi
Ta ce ta amince da tabbacin da ya ba ta saboda ta san yadda kungiyoyi masu zaman kansu suke yi, in suka bada irin wannan aiki, kuma suna biya bayan an kammala aikin.
Daga nan sai ta saki zuciyarta ta ci gaba da bin umurnin mutumin ta samo ma’aikata ta suka kwana suna aikin yin abinci.
Ta ce da suka kammala sai ta ƙira mutumin da nufin ta san waɗanda za su karɓi abincin, sai ya ce ta jira yana jiran a ba shi umurni tukuna.
“Bayan karfe 1 na rana ban ji ɗuriyarsa ba, sai na tafi ofishinsa, ya ce in jira yana jiran umarni.
“Bayan uku na yamma na fara ƙiran sa sau da yawa, amma ba ya ɗauka.
“Da muka je ofishinsa da mijina da misalin karfe biyar na yamma, sai aka ce mana ba ya nan.
“Tun daga lokacin ya ƙi ɗaukar wayata har ƙarfe biyar na yammaci.”
Hajiya A’isha ta ce ta yi matukar kaɗuwa da lamarin domin ta karɓi basussuka ne ta yi abincin.
Da ta kasa samun mutumin, sai ta shiga kafafen sada zumunta tana neman taimako.
Ta ce “Kwamishiniyar jin ƙai da bada agaji na Jihar Bauchj Hajiya Hajara Yakubu Wanka ta ƙira ni inda ta ce Gwamna ya ga bidiyona a intanet kuma ya umarce ta da ta biya ni diyya.
“Ina godiya ga Gwamna Bala Mohammed kan matakin da ya ɗauka na ceto ni cikin gaggawa.”
Hajiya Aisha ta ce gwamnati ta biya kuɗin da ta sayi kayan Naira miliyan 7.5 ba, kuma ta karɓi abincin aka rarraba shi wa masu bukata.
Da yake mayar da martani kan lamarin, babban sakatare a ma’aikatar, Alhaji Shuaibu Alhaji Muhammad, ya bayyana cewa asalin kuɗin kwangilar naira miliyan 13 ne, amma gwamnatin jihar ta biya diyya na ainihin kuɗin kayan abinci da Hajiya Aisha ta saya.
Wani abu daya ja hankalin jama’a shi ne Hajiya Aisha ta zabi kada ta bayyana sunan mutumin da ya yaudare ta, duk da cewa ta yi wa jami’an tsaro cikakken bayani.
Ta kuma gargaɗi jama’a game da masu zamba a asusun banki da za su ce za su rika neman tallafi da sunanta.
Kalli bidiyo a nan: