Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

0
459
Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Wannan mutumin ɗan Ghana ne, talaka ne, kuma yana zaune a ƙauye ne a wajen birni. Shekaru kaɗan da suka gabata wani jirgin sama mara matuƙi mallakar kamfanin dillancin labaran Turkiyya ya faɗo kusa da gidansa.

Da ‘yan jaridar ƙasar Turkiyya suka zo neman jirginsu, sai suka iske mutumin riƙe da jirgin mara matuƙi a hannunsa. Ya ce ga abinku, cikin raha ya tambaye su “kuna da wanda ya fi shi girma wanda zai kai ni aikin Hajji?”

Sai kuwa wani ɗan jarida ya wallafa labarin, daga nan kuma gwamnatin Turkiyya ta yanke shawarar tura mutumin Hajji ba tare da ya kashe ko sisin kwabonsa ba, wato dai duk abin da ake buƙata a tafiyar za ta biya masa.

KU KUMA KARANTA: Labarin Haji Hassan na ƙasar Iran

Ga shi nan dai a bana Allah Ya cika masa burinsa ya je Makkah domin aikin Hajjinsa.

Darasin labarin: Idan Allah ya ƙira ka zuwa Makkah, zai yi amfani da duk wani abu da duk wanda zai sa tafiyarka ta yiwu.
Allah ne mafificin tsari.

Leave a Reply