Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragi da Fenerbahçe

0
76
Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragi da Fenerbahce

Mourinho ya sanya hannu kan kwantiragi da Fenerbahçe

Ƙungiyar Fenerbahçe ta Turkiyya ta sanya hannu kan yarjejeniya da koci ɗan asalin Portugal, Jose Mourinho.

Shugabannin ƙungiyar Fenerbahçe ta Turkiyya sun cim ma yarjejeniyar aiki ta shekara biyu da Jose Mourinho.

Jagororin kulob ɗin da ke buga wasa a gasar Super Lig ta Turkiyya, Ali Koç da Mario Branco, sun gudanar da tattaunawar da kocin ɗan asalin Portugal.

Sun cim ma kyakkyawar matsaya a tattaunawarsu da Mourinho don ya zama daraktan wasanni na ƙungiyar.

Za a rattaba hannu a hukumance bayan taron ido-da-ido tsakanin Mourinho da shugabansu Ali Koç a ƙarshen mako.

KU KUMA KARANTA: Jose Mourinho ya nuna sabon tattoo na bikin murnar sharewarsa ta musamman ta Turai

Ƙungiyar Fenerbahçe na ci gaba da shirye-shiryen share fagen kakar baɗi, bayan ta kammala kakar bana a mataki na biyu a gasar Super League da maki 99.

Shugaban hukumar ƙungiyar, Ali Koç, wanda yake takarar shugabancin ƙungiyar a Taron Babban Zauren ƙungiyar, ba zai ci gaba ba tare da İsmail Kartal a matsayin kocin babbar tawagar ta A a sabuwar kaka.

Shugaba Ali Koç da Daraktan Wasanni na ƙungiyar Mario Branco, sun sanar da İsmail Kartal game da hukunci kan wannan batun. Kulob ɗin zai sanar a hukumance cikin kwana ɗaya zuwa biyu masu zuwa.

A wajen shugaban ƙungiyar Ali Koç, da ma ɗan takarar shugabanci Aziz Yıldırım, Jose Mourinho ne ke kan gaba a jerin waɗanda ake son ɗauko wa don jagorantar Fenerbahçe.

Mourinho ya bibiyi wasan ƙungiyar na baya-bayan nan a gasar, ya kuma ɗauki bayanai game da yanayin tawagar.

Kuma rahotanni sun nuna cewa koci ya samu bayanai game da kulob ɗin da birnin daga wajen ‘yan wasan da suka taɓa buga wasa a Fenerbahçe.

Leave a Reply