Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

0
84
Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin jirgin samanta

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin sufurin jirgin samanta na Air Nigeria, har sai Baba ta gani.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, ne ya sanar da hakan yayin taron Ministoci na cika shekarar Tinubu, guda a kan mulkin ƙasar.

Ya ce, matakin ya zo ne, lura da cewa kamfanin a ko da yaushe yunkurin yin amfani da jiragen saman wasu ƙasashen waje ya ke a matsayin na ta.

Idan za a iya tunawa, a shekarar 2023 ne, ma’aikatar sufurin jiragen sama, ƙarƙashin jagorancin tsohon ministan sufuri, Hadi Sirika, ta ƙaddamar da kamfanin jirgin mallakin Najeriya, wato Nigerian Air kwanaki uku kafin ƙarshen wa’adin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Lamarin dai ya yanwo cece-kuce a tsakanin al’ummar ƙasar, la’akhari da yadda daga bisani aka gane cewa akwai kuskunda a cikin batun.

Leave a Reply