Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

0
77
Sojojin Isra'ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Sojojin Isra’ila sun sanar da cewa an yi musayar wuta da dakarun Masar a ranar Litinin a kan iyakar Rafah da ke tsakanin Masar da zirin Gaza.

“A ‘yan sa’o’i da suka gabata, an yi harbi a kan iyakar kasar Masar, ana gudanar da bincike kan lamarin. Ana tattaunawa da ɓangaren Masar,” in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

KU KUMA KARANTA: Kotun duniya ta umurci Isra’ila ta dakatar da kai farmaki a Rafah

Kafar yaɗa labaran Isra’ila ta KAN ta ce an kashe wani sojan Masar a harin da aka kai.

Leave a Reply