Shekara ɗaya tayi wa Tinubu kaɗan ya warware matsalolin da ya gada – Sarki Sanusi

0
113

Shekara ɗaya tayi wa Tinubu kaɗan ya warware matsalolin da ya gada – Sarki Sanusi

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammadu Sanusi ll, ya ce dole ne ‘yan Najeriya su kasance sun yi nazari kada su yi tsammanin shugaba Bola Tinubu zai magance matsalolin ƙasar nan a shekara guda.

Matakin da gwamnatocin tarayya da na Jihohi suka yi, domin magance illar cire tallafin mai bai haifar da wani gagarumin tasiri ga ɗimbim al’ummar ƙasar nan ba.

Sanusi, ya yi imanin cewa manufofin gwamnatin Tinubu dole ne su kasance a halin da ake ciki.

“Yana da muhimmanci mu faɗa wa kan mu gaskiya matsayinmu na ‘yan Najeriya mu kasance mun faɗawa kan mu gaskiya” in ji Sanusi a jiya Alhamis yayin da yake gabatar da wani muhimmin jawabi a taron koli na tattalin arziƙi da zuba jari na jihar Rivers 2024 a Port Harcourt a jihar Rivers.

KU KUMA KARANTA:CISLAC ta yi ƙira ga ɗaukar matakin gaggawa wurin an samu zaman lafiya a masarautar Kano

Malam Sanusi ya ƙara da cewa, “Ɓarnar da aka yi a shekaru goma ba zai yi wu a gyara ta a watanni shida ko shekara guda ba,” yayin da yake magana kan matsalar tattalin arziƙi da cire tallafin man fetur ya haifar.

“Muna buƙatar fahimtar cewa wasu abubuwa masu wahala za su ɗauki lokaci don yin tasiri a gyaran tattalin arziƙi. Zai ɗauki ɗan lokaci kaɗan kafin mu ga canji, amma waɗannan shawarwarin sun zama dole a gare mu don ceton tattalin arzikin, ”in ji shi.

Sanusi, ya ce yana fatan wahalar za ta kasance taƙaitacciya, kuma nan ba da jimawa ba za a mayar da Najeriya kan turbar ci gaban tattalin arziki.

Leave a Reply