Connect with us

Labarai

CISLAC ta yi ƙira ga ɗaukar matakin gaggawa wurin an samu zaman lafiya a masarautar Kano

Published

on

CISLAC ta yi ƙira ga ɗaukar matakin gaggawa wurin an samu zaman lafiya a masarautar Kano

Cibiyar inganta aikin majalisar da rajin yaƙi da cin hanci da rasahwa ta CISLAC, ta bayyana matuƙar damuwa ga dambarwar dake faruwa na sake maida Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu a kan karagar mulki, da kuma sauƙe Alhaji Aminu Ado Bayero.

CISLAC ta yi kashedi cewa abubuwan dake faruwa na barazanar jefa jihar Kano cikin rikici da tashin hankali, lamarin da zai kawo rashin zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya.

Babban Daraktan CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi gargaɗin da kakkausar murya kan duk wani yunƙuri na amfani da lamarin wajen ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Kano. Ya ce, “Ana kallon irin waɗannan ayyuka a matsayin rashin tunani da kuma takala wanda zai iya wargaza tarihin siyasar Kano na sama da shekaru 1,000.”

KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya ba da umarnin kama Aminu Ado Bayero

CISLAC ta lura cewa hukuncin kotu mai tattare da cece-ke-ce da jami’an tsaro suka dogara da shi ya taimaka wajen dawo da Sarki Aminu Bayero. Alƙalin da ya zartar da hukunacin yanzu haka ba shi a cikin ƙasar kana ba shi kan aikinsa.

“Halin da ake ciki ya haifar da muhimman batutuwa a kan halasci da cancantar hukuncin kotun, in ji Rafsanjani.” Dogaro da abin da CISLAC ta kwatanta da ‘umarnin kotun cin zali’ wurin tura ‘yansanda da jami’an tsaro suka mamaye jihar Kano ya yi matuƙar tada hankali da kuma rura fitina.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, gwamnatin jihar na da hurumin nadawa da kuma tabbatar da sarakunan gargajiya, ciki har da babban Sarkin. “Rafsanjani ya jaddada cewa ba za a lamunta da duk wani yunƙuri na ƙwace wannan hurumi da kuma jefa jihar cikin rikici ba. “CISLAC ta yi imani cewa Gwamnatin Jihar Kano tana da ‘yancin shawo kan matsalolin dake addabar masarautunta kuma dole ne a mutunta wannan ‘yancin domin kaucewa faɗawa rikici.”

CISLAC ta yi ƙira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kar ya yarda da duk wani yunƙuri na ‘yan siyasa dake neman kawo cikas ga zaman lafiya da haɗin kai a jihar Kano. “Bai kamata gwamnatin tarayya ta bari a yi amfani da ita a matsayin makamin da za a cimma muradun siyasa kana a ƙara dagula zaman lafiyar jihar da yankin, Rafsanjani yana kashedi.”

A matsayinta na mai fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya da zaman lafiya, CISLAC ta tsaya tsayin daka wajen yin Allah wadai da duk wani nau’i na tashin hankali da cin zarafin hukumomi a jihar Kano. Ƙungiyar ta yi ƙira ga dukkan muhimman hukumomin da su ba da fifiko kan tattaunawa da neman hanyoyin da suka dace wajen magance wannan rikici.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like